ABNA24 : Ma’aikatar tsaron ƙasar Mozambique ɗin ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwar da ta fitar inda ta ce haɗin gwuiwan sojojin ƙasashen biyu sun kori ‘yan tawayen da suke riƙe da birnin mai tashar jiragen ruwa mafi muhimmanci a yankin.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Maputo, babban birnin ƙasar ta Mozambique, kakakin Ma’aikatar tsaron Kanar Omar Saranga ya ce a halin yanzu dai dakarun gwamnatin suna riƙe da irkon gine-ginen gwamnati, tashar jiragen ruwan, filin jirgin sama, asibiti da kuma sauran wajaje masu muhimmanci na birnin.
Ana ganin kama ƙwace wannan birnin daga hannun ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadin a matsayin wani gagarumin rashin nasara ga mayaƙan waɗanda suke da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh ko kuma ISIS
A watan da ya gabata ne gwamnatin Rwanda ta tura kimanin sojoji 1000 zuwa Mozambique don taimakawa dakarun ƙasar da kuma sauran waɗanda ƙasashen ƙungiyar ci gaban ƙasashen Kudancin Afirka SADC suka tura ƙasar don faɗa da masu ikirarin jihadin da suka ƙaddamar da hare-harensu tun daga watan Oktoban 2017.
342/